Friday, December 5
Shadow

Wanene matashi

Matashi yana nufin mutum me karancin shekaru, kakkarfa, wanda bai kammala fahimtar menene rayuwa ba.

Yawanci ana alakanta mutane maza da mata dake tsakanin shekaru 15 zuwa 25 da matasa.

Saidai a wani kaulin, wasu sun ce har dan shekaru 30, wasu ma sun ce kai dan shekaru 40 ka za’a iya kiranshi da matashi.

Duk da yake cewa dan shekaru 30 zuwa 40 za’a iya cewa sun fahimci menene rayuwa, amma daya daga cikin abinda ake fassara kalmar matashi dashi akwai karfi.

Kuma dan shekaru 30 zuwa 40 indai ba yana da wata zaunanniyar cuta ba, zaka ga da karfinsa.

Karanta Wannan  Al'ummar Kano Sun Zargi 'Yansanda Da Yunƙurin Sanya Dokar Ta-baci Kan Gayyatar Sarki Sunusi

Kuma manyan mutane zasu iya kiran kanana da matasa.

Misali dan shekaru 60 zai iya kiran dan shekaru 30 zuwa 40 da matashi.

Dan shekaru 40 zai iya kiran dan shekaru 15 zuwa 25 da matashi.

Dan haka kalmar matashi na da yalwa amma wadda aka fi aminta da ita itace mutanen dake tsakanin shekaru 15 zuwa 25.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *