Wani abu da ba’a san ko menene ba ya daki Jirgin saman Mataimakin Shugaban kasa,Kashim Shettima.
Hakan yasa dole ya fasa halartar taron Commonwealth da yayi shirin zuwa.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya wakilta Kashim Shettima ya halarci taron a madadinsa amma hakan bai yiyu ba.
Sanarwar hakan ta zo ne daga bakin me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar yada labarai, Bayo Onanuga.
Lamarin ya farune a yayin da Shettima ya tsaya a filin Jirgin sama na JFK dake birnin New York dan hutawa. A yanzu sanarwar tace tawagar ministocin da suka yi gaba ne zasu wakilci Najeriya a wajan taron.
Jirgin dai na Kashim Shettima yana can ana gyaransa.