
Rahotanni sun bayyana cewa, wani abu me kama da bam ya fashe a unguwar Abakpa dake kusa da tsohuwar NDA a cikin garin Kaduna.
Abin yayi sanadiyyar mutuwar yara biyu,daya sunansa Imam me shekaru 13 dayan kuma Narin me shekaru 6.
Lamarin ya farune a ranar Talata, 22 ga watan Afrilu.
Tuni jami’an tsaro suka kai dauki wajan.
Zuwa yanzu dai ba’a tabbatar da meme ya fashe ba.
Wani shaida yace yana cikin wanda ya ji fashewar abin inda ya fito dag ya ga meme sai ya ga Imam ya jikkata, yace kamin su kaishi Asibiti ya rasu.
Hakanan lamarin yayi sanadiyyar jikkatar mutane 3.