Friday, September 11
Shadow

Wani abu me kama da Bam ya fashe a Kaduna, Mutane 2 sun mutu, 3 sun jikkata

Rahotanni sun bayyana cewa, wani abu me kama da bam ya fashe a unguwar Abakpa dake kusa da tsohuwar NDA a cikin garin Kaduna.

Abin yayi sanadiyyar mutuwar yara biyu,daya sunansa Imam me shekaru 13 dayan kuma Narin me shekaru 6.

Lamarin ya farune a ranar Talata, 22 ga watan Afrilu.

Tuni jami’an tsaro suka kai dauki wajan.

Zuwa yanzu dai ba’a tabbatar da meme ya fashe ba.

Wani shaida yace yana cikin wanda ya ji fashewar abin inda ya fito dag ya ga meme sai ya ga Imam ya jikkata, yace kamin su kaishi Asibiti ya rasu.

Hakanan lamarin yayi sanadiyyar jikkatar mutane 3.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Bayan "wulakancin" Matar Shugaban kasa, Remi Tinubu tawa Gwamnan Jihar Osun, An kuma ga abinda tawa matar tsohon shugaban kasa, Patience Jonathan wanda wasu ke cewa yama fi abinda tawa Gwamnan Osun Muni

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *