
Wani Alhaji ya bayyana a kafafen sada zumunta inda yake sayawa ‘yan mata Pizza ta Naira 25,000.
Lamarin dai ya farane bayan da wata Budurwa ta koka da cewa, wai ace yanzu Pizza farashinta ya kai Naira 25,000.
Ya bukaci ta tura masa bayanan bankinta dan ya bata kudin ta saya.
Wannan abu yasa wasu suka rika kiransa da sunaye kala-kala saidai abin bai masa dadi ba inda shima ya rika mayar da raddi.