Wani guri da ake kira da Jehova Allah a Legas ya bayyana
inda musulmai da Kiristoci ke haduwa su yi Ibada.
Gurin ana karatun Qur’ani a cikin sa sannan ana wakewake da addu’a irin ta Kiristanci.
Lamarin ya baiwa mutane mamaki sosai musamman ganin yanda ba kasafai aka cika samun irin wannan hadaka ba a kasarnan.
Rahoton jaridar Punchng yace an gina wajan ne shekaru 12 da suka gabata dan samar da hadin kai tsakanin musulmai da kirista.