Wani mutum ya kashe kansa ranar Juma’a a yankin Enyenkorin na garin Ilorin dake jihar Kwara.
Mutumin ya kashe kansa ne ta hanyar rataya a jikin Bishiya.
Wani mutum da ya shaida lamarin yace sun iske wata takarda a jikin mutumin inda ya rubuta lambar dan uwansa da matarsa a jihar Gombe.
Tuni dai ‘yansanda suka isa wajan inda suka kai gawar mamacin mutuware.