Saturday, March 15
Shadow

Wani mùtùm ya mùtù a kokarin dakko wayarsa data fada rijiya

Wani mutum me suna Sunday Jimoh a jihar Ogun ya mutu a kokarin dakko wayarsa data fada rijiya.

Mutumin me shekaru 31 na zaunene a Laditan dake yankin Oja-Odan na jihar, kuma lamarin ya farune ranar 22 ga watan Fabrairu da misalin karfe 10: 00 na safe.

Kakakin ‘yansandan jihar, CSP Omolola Odutola ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi.

Wata mata Kabiru Aladeshayi Ayigbere ce ta kaiwa ‘Yansandan korafi akan lamarin inda tace an yi kokarin hana Jimoh shiga rijiyar amma ya nace sai ya shiga.

Omolola yace sun je wajan inda aka ciro gawar mamacin kuma an yi bincike babu wata alamar duka a jikinsa wanda hakan ya tabbatar da cewa mutuwa yayi ta Allah da Annabi.

Karanta Wannan  Mutane 171 sun mutu bayan hadarin jirgin sama

Danginsa sun bukaci a basu gawarsa su binneshi kamar yanda addinin musulunci ya tanada kuma an basu.

Hukumar ‘yansandan jihar ta jawo hankalin mutane su daina saka kansu cikin irin wannan matsala da zata kai ga rasa rai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *