
Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu Sarki ya dauki hankula sosai a wajan bikin Arewa Turnup da Rahama Sadau ta shirya.
Babban abinda ya dauki hankalin mutane shine yanda Ali Nuhu da Rahama Sadau suka rika rawa tare da Umar M. Shariff.
Ali Nuhu ya saki jikinsa sosai yayi rawa ba tare da shakka ba.
Hakan yasa mutane ke cewa wai yaushe zai girma ne?
Ali Nuhu dai ya saba rawa irin haka, saidai mutane sun kasa sabawa da ganinsa yana rawar inda a duk sanda yayi sai an yi magana.