Bashir Ahmad yayi magana kan jita-jitar auren Shiekh Pantami da Aisha Buhari

Wannan ba labari ba ne da ya kamata ma a tsaya ana ƙoƙarin ƙaryata shi, domin duk wani mai hankali ba zai ɗauke shi da muhimmanci ba. Sai dai tunda har yanzu wasu na ci gaba da yaɗa wannan jita jitar, ya zama dole a fayyace gaskiya. Labarin da wasu ke yadawa cewa Hajiya Aisha Buhari ta amince za ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ce tsagwaronta. Babu ko ƙwayar gaskiya a cikinsa kwata-kwata. -inji Bashir Ahmad tsohon hadimin margayi Buhari
Me zaku ce?
Daga Kafar Ayau News