
Wani bawan Allah ya koka dacewa a lokacin Janar Christopher Musa na shugaban sojojin Najeriya, sau 3 ana jefawa musulman da basu ji ba basu gani ba bama-bamai da sunan Kuskure.
Ya ce an jefawa masu Maulidi Bam a Tudun Biri ranar 3 ga watan Disamba 2023 inda mutane 126 suka rasa rayukansu.
Hakanan yace akwai wani kauye a Sokoto da shima aka jefawa bama-bamai mutane 10 suka rasa rayukansi.
Sannan yace ranar 13 ga Janairun 2025 ma an jefawa mutane bama-bamai a Zurmi jihar Zamfara inda mutane 16 suka rasa rayukansu.
Yace saidai tun bayan sauke Janar Christopher Musa ba’a sake samun irin wannan matsalar ba.
Yace nadashi Minista rashin girmama Musulmai ne kuma ya sa musulmai da yawa sun kadu, inda yayi fatan Sanatoci Musulmai ba zasu amince dashi ba a matsayin sabon ministan tsaro.