Tuesday, May 19
Shadow

Wani ya koka da cewa a lokacin Christopher Musa na shugaban sojojin Najeriya, sau 3 ana Jèfà Bàmà-Bàmàì akan Musulmai wanda basu ji ba basu gani ba da sunan kuskure

Wani bawan Allah ya koka dacewa a lokacin Janar Christopher Musa na shugaban sojojin Najeriya, sau 3 ana jefawa musulman da basu ji ba basu gani ba bama-bamai da sunan Kuskure.

Ya ce an jefawa masu Maulidi Bam a Tudun Biri ranar 3 ga watan Disamba 2023 inda mutane 126 suka rasa rayukansu.

Hakanan yace akwai wani kauye a Sokoto da shima aka jefawa bama-bamai mutane 10 suka rasa rayukansi.

Sannan yace ranar 13 ga Janairun 2025 ma an jefawa mutane bama-bamai a Zurmi jihar Zamfara inda mutane 16 suka rasa rayukansu.

Yace saidai tun bayan sauke Janar Christopher Musa ba’a sake samun irin wannan matsalar ba.

Karanta Wannan  Najeriya ce kan gaba a yawan fitar da man fetur a Afirka cikin watan Mayu - OPEC

Yace nadashi Minista rashin girmama Musulmai ne kuma ya sa musulmai da yawa sun kadu, inda yayi fatan Sanatoci Musulmai ba zasu amince dashi ba a matsayin sabon ministan tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *