
Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa a wannan shekarar ta 2026, ‘yan Najeriya su yi tsammanin samun ci gaba sosai.
Ya bayyana hakane a wajan taron murnar kaiwar kasuwar hannun jarin Najeriya darajar Naira Tiriliyan 100.
Ya bayyana cewa, hakan zai kara jawo hankalin masu zuba hannun jari a Najeriya.