
A yayin da siyasar Najeriya ta mayar da hankali kan dakatar da gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara, manyan ‘yan Adawa na ta Allah wadai da wannan mataki na shugaban kasa.
Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasiru El-Rufai, da sauran manyan ‘yan Adawa duk sun fito suna ta Allah wadai da wannan mataki, saidai ba’a ji duriyar Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ba.
Daya daga cikin wadanda suka bayyana irin wannan ra’ayi shine Comrade Adnan.
Ya bayyana cewa, duk da shirun Kwankwaso akan lamari irin wannan amma haka mutane ke kiransa da Jagora.
Abin dai jira a gani shine ko Kwankwaso zai yi magana akan lamarin.