
Hukumomin ƴansanda a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya sun cafke wata mata bisa zarginta da kashe kishiyarta ta hanyar zuba mata ruwan zafi.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Buju da ke ƙaramar hukumar Dutse babban birnin jihar Jigawa, kuma bayanai na cewa matar ta rasa ranta ne sakamakon rashin jituwar da ta kaure tsakaninta da abokiyar zamanta.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam ya shaida wa BBC cewa matar ‘yar shekara 20 ta watsa wa abokiyar zamanta tafasasshen ruwan zafi ne, sakamakon taƙaddamar da ta kaure tsakaninsu.
SP Shi’isu Adam ya ce marigayiyar ta samu mummunan ƙuna, inda aka kai ta asibiti daga baya kuma ta rasu a can.
Mai unguwar ƙauyen, Malam Kabiru Abbas ya shaida wa BBC cewa bayan ƙura ta lafa, wadda aka watsa wa ruwan zafin, kafin ta rasu ta kai masa ƙorafi, inda ya ba ta shawarar zuwa ofishin ƴansanda domin shigar da ƙorafinta.
Ya ƙara da cewa sai da ta shafe mako guda tana fama da jinya, kafin ta rasu, sakamakon munanna raunukan da ta ji saboda ƙunar.
Kakakin ƴansandan ya ce tuni suka kammala tattara bayanai kuma domin tura ta kotu.