Sunday, March 23
Shadow

El-Rufai ya bude shafin TikTok, ya samu mabiya 200,000 cikin Awa 24

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bude shafi a dandalin sada zumunta na TikTok.

Cikin awa 24 kacal da budewa, El-Rufai ya samu sama da mabiya 200,000, yayin da bidiyon sanarwarsa ya tara masu kallo miliyan 1.9 da kuma sharhi (Comment )sama da 21,000.

A cikin bidiyon, El-Rufai ya bayyana cewa shafinsa na TikTok zai mayar da hankali kan ra’ayoyinsa a siyasa da kuma sabuwar jam’iyyarsa, SDP.

“Wannan shine kawai shafina na gaskiya a TikTok. Ku biyo ni domin kallon bidiyo, yin sharhi da tattaunawa kan siyasar Najeriya da ayyukan sabuwar jam’iyyarmu, SDP. Maraba da ku,” in ji shi.

Karanta Wannan  Yadda ake dambun kifi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *