
Wata Kungiya daga yankin Arewa maso gabas ta yi kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya ajiye Kashim Shettima ya dauki Yakubu Dogara a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2027.
Kungiyar me suna the Coalition of APC Support Groups in the North-East ta bayyana hakane a zaman data gudanar a ranar Litinin a jihar Gombe.
Kungiyar tace Yakubu Dogara ne wanda yafi dacewa ya zama mataimakin shugaban kasa a shekarar 2027.
Tace zata nada wakilai da zasu jagoranci mutane zuwa ganin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a Abuja dan isar masa da sakonsu.