
Dan Gwagwarmaya, Mahadi Shehu ya bayyana mutanen da yake tsammanin zasu yi takara a zaben shekarar 2027 da abokan takararsu.
Ya rubuta hakane a shafinsa na X inda ya bayyana ‘yan takarar da yake tsammanin zasu yi takara a kowacw jam’iyya.
A jam’iyyar APC yace akwai yiyuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai yi takara da tsohon gwamnan jihar Borno, Modu Ali Sheriff, ko Yakubu Dogara, ko babban Fasto, Mathew Hassan Kuka.
A jam’iyyar ADC kuwa, yace akwai yiyuwar Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi ne zasu yi takara a 2027.
A Labour Party kuwa yace Peter Obi da Ko dai tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, Datti Baba Ahmad, ko Aminu Waziri Tambuwal.
A PDP kuwa yace akwai yiyuwar, Goodluck Jonathan su yi takara tare da Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ko ya dauki Kwankwaso a matsayin mataimaki ko kuma Seyi Makinde da Bala Mohammed ko kuma Wike da Kwankwaso.