
Dan takarar Gwamnan jihar Kebbi a jam’iyyar APC, Mallam Salihu Isa Nataro ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar ya yi kokarin mayar da tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai jam’iyyar APC.
Yace masa, El-Rufai na da karfin fada aji sosai musamman a siyasar Arewa maso yamma.
Yace kuma komawarsa jam’iyyar APC zata sa talakawa da yawa su dawo suna son Tinubu din.
Yace kada a bari rashin jituwa tsakanin shuwagabannin jam’iyya da El-Rufai yasa a kyaleshi.
Ya bayyana cewa ya kamata a yi kokari El-Rufai ya koma APC kamin zaben 2027.