
Rahotanni sun bayyana cewa, Naira Biliyan 200 da EFCC ke zargin Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami da sacewa, ya samesu ne daga kudaden bashin da babban bankin Najeriya, CBN ya baiwa manoma bashi lokacin Buhari.
Da kuma kudin Abacaha da aka dawo dasu Najeriya da kuma kudin Paris Club watau bashin da Gwamnatin Tarayya da gwamnoni suka ciwo.
Kafar The Cable tace ta samu cewa Abubakar Malami ya sa matarsa me suna Hajiya Bashir Asabe ta ci bashin na manoma har Naira Biliyan 4 wanda kuma bata biya ba.
A yanzu dai EFCC sun sakata cikin wadanda za’a gurfanar dasu a gaban kotun tare, a baya dai Hutudole ya kawo muku cewa akwai dan Abubakar Malami da shima yanzu EFCC ke tuhuma.
A bangaren Kudaden Abacha da aka karbo, lauyoyi turawa aka dauka suka yi aiki, amma rahotan yace Abubakar Malami shima ya dauki sabbin lauyoyi duk da cewa an kammala komai kudin kawai za’a bayar amma Malami yasa Lauyoyin suka yi aikin Boge aka biyasu dala Miliyan $16