Wednesday, January 15
Shadow

Wata Sabuwa: Ana zargin kwaikwayar sa hannun Babban alkalin kotun Kano aka yi aka fitar da hukuncin kotu na karya wanda yace a sauke Sarki Sanusi II daga kujerar sarautar Kano, Kalli Hotunan dake tabbatar da hakan

Wasu alamu sun nuna cewa ga dukkan mai yiyuwa kwaikwakayar sa hannun babban alkalin kotun tarayya dake Kano aka yi aka fitar da hukuncin kotu na karya da yace a cire sarki Muhammad Sanusi II daga kan kujerar sarautar Kano.

A wani bincike da Kafar Daily Nigerian ta yi, ta gano cewa sa hannun da aka gani a takardar data dakatar da sarkin ta banbanta da sauran sahannun da alkalin ya saba yi.

Kuma a baya, Alkalin yakan saka hannu a duka takardun hukunci ne amma a na hukuncin da ya sauke sarkin, a takardar karshe ce kawai aka saka hannun.

Hakanan kuma Akwai wanda ake tuhuma a takardar kotun su 8 amma cikinsu babu wanda baiwa kwafin takardar sai kwamishinan ‘yansandan jihar kadai.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Kar ka jefa Kano cikin rikicin da ba za a iya gujewa ba, wasu Malaman Musulunci sun gargaɗi Gwamna Abba Kabir Yusuf

Wannan yasa ake zargin cewa takardar ta boge ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *