
Duk rawar kai da iyayin Kwankwaso ba zai gaji ƙuri’un Buhari miliyan 12 ba -inji Umahi
Ministan Ayyuka, David Umahi, ya ce yunkurin Rabiu Kwankwaso na neman ya gaji kuri’un Buhari ba zai yiwu ba. Umahi ya karyata zargin cewa Tinubu ya watsar da yankin Arewa.
Ministan ya nemi Kwankwaso ya janye kalaman sa, yana jaddada cewa Tinubu na mulki da adalci kuma babu wariya.
Me zaku ce?