Gwamnatin jihar Enugu ta sanar da saka haraji akan gawarwakin da aka ajiye a mutuwaren dake Asibitocin jihar.
Saidai gwamnatin tace ba da niyyar tatsar mutane da tara kudade barkatai bane ta aikata hakan.
Shugaban hukumar tara kudaden shiga na jihar, Mr Emmanuel Nnamani
Ya yi karin haske kan lamarin inda yace duk gawar da aka kai mutuware a jihar kuma ‘yan uwanta basu dauketa ba har ta wuce awanni 24 watau kwana daya to duk rana za’a rika biya mata harajin Naira 40 har zuwa ranar da za’a dauketa daga mutuwaren.
Yace wannan ba sabuwar haraji bace kuma an dauki matakinne dan hana mutane kai gawarwakinsu mutuware a jihar.