Friday, December 5
Shadow

Wata Sabuwa, Rahotanni daga (ICIR) sun ce Shugaba Tinubu bashi da Lafiya rabon da a ganshi a office tun 1 ga watan Augusta

Kafar ICIR tace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bashi lafiya kuma ana shirin fita dashi kasar waje neman magani.

Saidai me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya musanta hakan inda yace shugaban na nan qalau.

Rabon da a ga shugaba Tinubu a bainar jama’a dai tun ranar 1 ga watan Augusta wanda hakan ne yasa ake rade-radin cewa bashi da lafiya.

Hakanan an dage zaman majalisar zartaswa wadda shugaban kasar ke jagorabta a fadarsa.

Kafar ta (ICIR) tace saboda rashin lafiyar ta shugaba Tinubu, ya nada mataimakinsa, Kashim Shettima ya jagoranci gudanar da ayyuka a madadinsa.

Saidai me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga yace shugaba Tinubu ya zabi ya rika aiki daga gidane, kuma babu wata matsala game da hakan.

Karanta Wannan  Ji yanda wata mata ta kàshè kishiyarta a Garin Daura na jihar Katsina

Game da daga zaman majalisar zartaswa kuwa, Bayo Onanuga yace a kowace rana za’a iya yin zaman majalisar zartaswa ba sai ranar Litinin ba kawai.

Ya kara da cewa ko a ranar 5 ga watan Augusta ya gana da shugaba Tinubu kuma lafiyarsa qalau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *