
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan Jam’iyyar ADC da yawane suka koma jam’iyyar NDC.
Shugaban jam’iyyar, Seriake Dickson ne ya karbesu a gidansa dake Abuja.
Tsohuwar ‘yar ADC da jam’iyyar ta dakatar, Amanda Pam ce ta jagoranci ‘yan jam’iyyar da yawa ciki hadda ‘yan Kwankwasiyya reshen Abuja suka koma jam’iyyar ta NDC.
Bayan su kuma akwai ‘yan labour Party da ‘yan SDP da suma suka koma jam’iyyar ta NDC.
Daga cikinsu akwai dakataccen shugaban ADC na AMAC, Omale Sule, da shugabar mata ta ADC reshen Abuja, Princess Gladys Ngozi, tsohon shugaban jam’iyyar ADC na Kuje, Godwin Onoya, da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC, Yusuf Adam da kuma tsohon shugaban matasa na jam’iyyar reshen Abuja, Aliyu Umar.
Sauran sune tsohon shugaban jam’iyyar SDP reshen Abuja, Nurudeen Bissallah, da kuma tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar Labour party reshen Abuja, Faruk Datsama.
A jawabinsa, Seriake Dickson ya bayyana cewa, komawar tasu NDC ba karamin daukaka jam’iyyar zai yi ba inda kuma yayi musu maraba.