Saturday, December 13
Shadow

Wata sabuwar Kungiya me cike da hadari da bata yadda da kowane irin addini ba ta bayyana a Kaduna

Hukumar kula da shige da fici a Najeriya, NIS ta bayyana samuwar wata kungiya me suna ACHAD a jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa Kungiyar na neman mabiya kuma bata yadda da wani addinin Musulunci ko na Kiristanci ba.

Hakanan an bayyana cewa kungiyar na safarar mutane musamman kananan yara.

An jawo hankalin mutane da su gaggauta sanar da hukumomi da zarar sun ga abinda basu ganemawa ba.

Karanta Wannan  Cikin sauki zan sake cin zabe a shekarar 2027, 'Yan Najeriya sun shaida kokarina, kar har Kungiyoyin Duniya irin su IMF sun jinjina min>>Shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *