
Rahotannin da hutudole ke samu na cewa a kalla mutane 9 ne suka mutu wasu suka jikkata bayan fashewar bam a tashar motar dake Maimalari a karamar hukumar Guzamala dake jihar Borno.
Rahoton yace an dasa bam dinne a tashar motar wnda daga baya ya tashi.
Lamarin ya farune da misalin karfe 11 a.m. na safiyar ranar Asabar.
Jaridar Punchng ta ruwaito kakakin majalisar jihar Borno, Hon. Abdulkarim Lawan ya tabbatar mata da faruwar lamarin.
Ya mika ta’aziyya ga iyalan mamatan inda yayi fatan samun sauki ga wadanda ke kwance a Asibiti.
Ya koka da yawaitar hare-haren kungiyoyi masu ikirarin Jìhàdì.