
Kristy Hallowell ‘yar shekaru 44 dake zaune a Greenwood Lake, New York City na kasar Amurka tace watansu 6 kenan basu da wutar Lantarki.
Ta bayyana cewa a watanni 6 na karshe na shekarar 2025 basu da wuta.
Tace ta rasa aikinta kuma an kara kudin wuta, dan haka ta kasa biya, tace gas ma basu dashi.
Tana zaunene ita da ‘ya’yanta da mahaifiyarta.
Inda tace dole saidai janareta suka rika amfani dashi.
Saidai an samu irin kungiyoyin masu taimakawa mutane sun biya mata rabin kudin kuma an sakw hada musu wutar amma har yanzu basu da gas.
Saidai tace har yanzu akwai yiyuwar a sake yanke mata wutar dan bashin da ake binta ya kai na sala $3000.