
Rahotanni sun ce manhajar WhatsApp da ake amfani da ita wajan Chatin da kasuwanci da sada zumunta zata daina aiki a cikin wayoyi kirar iPhone guda 3.
Masu irin wadannan wayoyi saidai ko su canja waya ko kuma su yi upgrading Operation System dinsu.
Kamfanin Meta wanda shi ke da WhatsApp yace daga yanzu wayoyi masu manhajar iOS 15.1 zuwa sama ne kawai zasu iya amfani da WhatsApp.
Hakan na nufin wayoyin iPhone 5s, iPhone 6, da iPhone 6 Plus duk ba zasu iya yin amfani da WhatsApp ba.
Kakakin WhatsApp ya shaida cewa a duk shekara sukan duba su ga wace waya ce ta fi tsufa wadda kuma babu mutane da yawa dake amfani da ita sai su dakatar da WhatsApp akanta.
Sunce wadannan wayoyi basu da manhajojin tsaro da ya kamata.
Wadannan wayoyi dai an yisu ne tsawon shekaru sama da 10 kuma kamfanin Apple yace sun tsufa