Monday, December 16
Shadow

Ya ake samun saurayi

Ana samun saurayi ta hanyoyi da yawa.

Wani karatu ne zai hadaku, ma’ana makaranta daya daga nan sai soyayya ta shiga tsakani.

Wani a hanya zai ganki ya ji kin yi masa, ya miki magana.

Wani a abin hawane zaku hadu dashi, misali mota ko adaidaita sahu, keke Napep zai ji yana sonki daga nan sai a fara soyayya.

Wani kafar sadarwar zamani watau social media ce zata hadaki dashi kuma har soyayya ta shiga tsakani.

Akwai hanyoyi da yawa na yin saurayi wanda mafi yawa ba shirya musu ake ba, a mafi yawan lokuta sai sanda baki tsammanin yin saurayi a lokacinne zaki sameshi.

Karanta Wannan  Maganin farin jinin samari

Abu daya kawai zaki rike shine tsafta da Addu’ar Allah ya hadaki da na gari.

A yanzu da zamani yazo, ana samun mace ma ta gayawa saurayi tana sonsa. Ko da baki furta da bakiba, idan kika ga Wanda ya miki akwai hanyoyi da zaki bi dan Jan hankalinsa.

Idan ya kasance kuna haduwa yau da gobe dashine zaki iya Jan hankalinsa ta hanyar hira da sauransu, idan kuma ganinshi ne kika yi, kika ji ya miki, zaki iya yi masa murmushi da zai ja hankalinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *