Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party, Peter Obi ya bayyana cewa, ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky da Obi Cubana ta je ta kama ‘yan siyasa masu sata.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV.
Yace idan da a yanzu gwamnati zata ce zata ciyar da mata kadai a Najeriya, saboda yunwar da ake ciki, maza da yawa zasu saka kayan mata su je karbar abincin.
Bobrisky dai yana can daure a gidan yari saboda lika kudi a wajan biki yayin da shi kuma Obi Cubana aka gurfanar dashi a gaban kotu shima saboda lika kudi.