Saturday, July 20
Shadow

Hoto: An kamashi da ka-wu-nan mutane 8 dan yin tsafi

Jami’an ‘yansanda a jihar Ondo sun kama wani matashi me suna Yusuf Adinoyi bayan samunsa da kawunan mutane 8.

Kwamishinan ‘yansandan jihar, Abayomi Oladipo, ya tabbatar da kamen inda yace an kama wanda ake zarginne ranar Litinin bayan an kafa shingen bincike.

Mutumin na kan hanyar zuwa Akure ne kamin aka tare motarsu wadda yayi kokarin tserewa amma aka bishi aka kamoshi.

Ya amsa laifinsa inda yace a baya yana sana’ar sayar da manja ne amma rashin lafiyar mahaifiyarsa tasa ya shiga harkar sayar da kawuna.

Yace wannan ne karo na 3 da yake son sayar da kawunan inda a farko ya sayar da guda 4, sannan ya sayar da guda 3 hakanan sai yanzu zai sayar da guda 8.

Karanta Wannan  MASU GARKUWA SUN BIDIGE MUTUM DAYA KAI MUSU KUDIN FANSAR YAN'UWAN SA NERA MILIYAN 16 DA MASHINA 3

Kwamishinan ‘yansandan yace za’a gurfanar dashi a kotu bayan kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *