AYA MAI SUGAR
INGREDIENTS :-Aya Kofi 4
Sugar Kofi Biyu
Gishiri Karamin Cokali
Flavour Karamin Cokali
Method:
Ki surfa aya ki wanke ta tas, ki xuba a tukunya ki soyata har sai kinga ta soyu, ki ajeta a side.
Ki zuba sugar 1 cup a tukunya da ruwa 1 cup da gishiri rabin karamin cokali ki dora a wuta ya dahu har sai sugar tayi danko ta fara kumfa sai ki zuba wannnan aya kina juyawa har sai ta hade. Ki juye a faranti. Ki dakko sauran sugar kiyi kamar na farko ki kuma xuba ita wannan ayar da kika sawa sugar da farko. In tayi ki juye a faranti ki zuba flavor ki juya.
Amfanin sa sugar sau biyu yafi haske ne in ba kya so kina iya sawa sau daya.