Monday, December 16
Shadow

Yadda ake danwake

YADDA AKE DANWAKE:

1/2 kwano garin alabo
3 cup flour
2 cup garin alkama
1 cup garin kuka
1 cup kanwa(Ajika da ruwa)
Ruwa(iya adadin kaurin da ake bukata)
Sinadaran hadawa(dandano)
Yaji(iya adadin da akeso)
Kwai(iya adadin da akeso)
Maggi
Soyayyen mai ko manja

Dafarko kina bukatar garin alabo(rogo),alkama da kuma flour,ni hadasu nake dukka guri daya sai a nikomin su,idan an. Niko sai na tankade na zuba flour iya adadin danakeso,da kuka na yi mixing dinshi sosai, ABUN jan hankali,wanan adadin danasaka adadi ne mai yawa gaskiya sbda na cin mutane goma 12 ne da,amma kamar cimar mutum 2 sai ayi amfani da alabo kopi 1 flour rabin kopi,alkama ma rabin kopi.

Karanta Wannan  Yadda ake miyar kuka

Dafarko bayan na tankade garina,na zuba garin kuka akai,na hadashi,sai na zuba jikakkiyar kanwa na akai

Sai na zuba ruwa iya adadin da zai hadamin(jug karami na roba acike) sai nayi amfani da muciya na hadashu sosai,gashinan bayan ya hadu.

Daganan sai ki nemo tukunyarki babba mai wadataccen fadi,ki zuba ruwa kmr rabin tukunyar,ki barshi ya tafaso,bayan ya tafaso saiki matso da kullin danwaken ki,da kuma ruwa a roba karami,saiki dankwali ruwan a hanunki sanan ki debo kullin kmr dai yadda yake a hoton nan.

Saiki jefa cikib ruwanki mai tafasa,(madaidata ko kanana,ko manya duk de yadda kike so)haka zakiyi tayi harsai kullin ki yakare, saiki rufe tukunyar da murfi ki jira shi ya juya(yatafaso)

Karanta Wannan  Yadda ake wainar shinkafa

Ni normally idan zanyi danwake tafasa sau hudu nake bari yayi,watau idan na rufe tukunyar yayiwo sama kamar zai zube sai na budeshi na saka matsami na juya sanan na rufe,haka haka har sau hudu,idan kuma baki gane hakan ba saiki debi ruwa a babbar roba,ki tsamo danwaken kadan a matsami ki zuba acikin ruwa,idan yayi kasa to ya dahu,amma idan yana yawo a saman ruwa(floating)to bai dahu ba gaskiya.

Gahinan na zuba yayi kasa,sai na kwashe dukka,na kara daureyewa da ruwa,shikenan sai na serving,zaki soya mai ki dafa kwai (kwai ra ayi ne),azuba mai askaa yaji da dunkulen maggi da kwai saici.

Karanta Wannan  Yadda ake dafa shinkafa jollof

Idan kika saba da danwake mai alabo gaskiya baza kiso ko wani irin danwake ba sai shi yana da dadi sosai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *