Wednesday, January 15
Shadow

Yadda ake gane cikin tagwaye

Babbar hanyar da ake gane cikin tagwaye shine ta yin gwaji.

Saidai akwai alamomi na al’ada wanda ake amfani dasu wajan gane cikin tagwaye bisa yanda aka saba gani a wajen masu haihuwarsu:

Wadannan alamu na cikin gwaye sune kamar haka:

Wadannan alamomi da zaku karanta sukan farune a kwanakin farko-farko na daukar ciki.

Za’a ji motsin ciki da wuri.

Za’a ji motsin ciki a bangarori daban-daban na cikin.

Cikin zai yi girma fiye da yanda aka saba gani a sauran cikkunan da ake dauka.

Nauyin jikin me cikin zai karu sosai.

A wajan gwaji, na’ura zata nuna zuciyoyi biyu na bugawa.

Wadannan sune alamomin dake nuna mace na dauke da Tagwaye, saidai kamar yanda muka fada a farko, babbar hanyar gane Tagwaue itace a yi gwaji.

Karanta Wannan  Addu'a ga mai ciki: Addu'ar saukin haihuwa

Mace zata iya rika jin wadannan alamomi a jikinta idan tana dauke da Tagwaye:

Zafin Nono.

Kasala.

Yawan Fitsari.

Son cin abinci fiye da da.

Zazzabin safe.

Ta yaya ake samun Tagwaye?

Yawanci ana samun tagwayene idan Allah yaso a samu, saidai bisa tarihi da yanda aka saba gani, an fi samun tagwaye ta wadannan hanyoyin:

Idan ya zamana akwai tarihin samun tagwaye a danginku.

Shekaru: Wanda suka haura shekara 35 sun fi samun damar haihuwar tagwaye.

Masu kiba sun fi samun damar haihuwar tagwaye.

Idan kin taba haihuwar ‘yan biyu, akwai yiyuwar zaki iya sake haihuwar wasu ‘yan biyun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *