Wednesday, January 15
Shadow

Yadda ake gane motsin ciki

Ana gane motsin ciki ne idan aka ji wani abu kamar filfilo a ciki.

Ana kuma iya jin kamar jaririn ya harba kafa.

Mace zata iya jin jijjiga.

Lokacin da jariri ke fara motsi a ciki:

Jariri na fara motsine a sati na 12 da daukar ciki amma ba zaki ji motsin ba.

Idan kin taba haihuwa, zaki iya jin motsin jaririn a sati na 16. Amma idan baki taba haihuwa ba, sai wajan sati na 20 kamin kiji motsin jaririn.

Saidai kowace mace akwai lokacin da take jin motsin jaririnta ba lallai ya zama lokaci guda ga kowace me ciki ba.

Zaki iya sa jaririnki yayi motsi:

Karanta Wannan  Yawan fitsari ga mai ciki

Masana sunce zaki iya sa jaririnki yayi motsi, idan kina son hakan, kawai zaki kwanta ne ta bangaren hagu ne.

Mafi yawanci, mace takan ji motsin jaririnta bayan ta ci abinci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *