AMFANIN SABAYA A JIKIN YA”MACE
Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Zai Taimaka Wajen Dawo da Halittan Da Allah Yai Mata Jikinta Nonon Bazai Zube Ba.
Na Biyu Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Jikinta Zaiyi Laushi Kamar Kwalabiya
Na Uku Idan Mace Tana Amfani Da Sabaya Da zarar ta Haihu Irin Ramar Da Mata Keyi Baza Tayi Ba
Kuma Ruwan Nononta Zai Qara Yawa Sannan Bazai Lalace Ba Kuma Yaron Data Haifa Allah Zai Kareshi Daga Dangin Cututtuka Sannan Hatta Magidanci Idan Yasha Yana Qara Masa Lafiya Da Kuma Kuzari a Jikinsa Hatta Wajen Kusantar Iyalinsa
ABUBUWAN DA AKE BUKATA WAJEN HADA SABAYA SUNE KAMAR HAKA:
*Al Kama 1Mudu
*Danyen Shinkafa 1Mudu
*Waken Suya 1Mudu
*Ridi ½Mudu
*Hulba ½Mudu
*Gyada Mai Bargo/Kamfala
*Madara
*Zuma
YA ZA’A HADASU SHINE:
Ridi Da Gyada Ana Hadasu Wuri Guda Ridi a Soyashi Yadda Ake Kantu, Gyadar A Soyata Yadda Ake Quli Quli, Shinkafa Da Alkama Ana Jiqasu Tsawon 5hour Sai a Shanya Da Laima a Jikin Sai a Hadasu Wuri Guda
Da Ridin Da Gyadar Da Al Kama Da Hulba Da Shinkafar Sai a Niqa Matarka Tin Tana Da Ciki Ya Kamata Ka Fara Bata Har Zuwa Haihuwa Kaga Yadda Zatai Da Yaronta Kuma Nononta Dana Shayarwa Ko Bata Shayarwa Bazai Canza Ba Da Ikon Allah
YADDA AKE SHANSA
Yadda Ake Dama Kunu Haka Ake Damashi Sai Dai Idan aka Zuba Ruwan Zafi Ana Iya Maidashi Kan Wuta
Cokali Uku a Rana ta Riqa Hadashi Da Zuma Da Madara Musamman Cikin Babban Cokali Idan Kuma Harda Magidancin Sai a Sanya Cokali Shida.