Wednesday, January 15
Shadow

Yadda ake miyar alayyahu

YADDA AKE MIYAR ALAYYAHU.

Abubuwan da ake bukata:
Alaiyaho
Dafaffafiyar ganda
Dafaffafen kayan ciki
Dafaffafen kwai (ki bare bawon)
Dafaffafen kifi
Ganyen kori
Albasa
Dafaffen markadadden kayan miya
Tumatir na gwangwani
Kayan kamshi
Sinadarin dandano
Man gyada
Lawashi

HADAWA:
Ki gyara Alayyahu, amma ba sai kin yanka ba, sai ki wanke da gishiri ki zuba mishi tafasashshe ruwan zafi ki rufe nadan wani lokaci; Sai ki tace a ajiye a gefe.

Dora tukunya a wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama-sama, sai ki kawo tumatir na gwangwani ki sa ki juya ki soya sama-sama.

Sai ki dauko dafaffafen kayan miya ki zuba a ciki ki juya ki rufe zuwa wani lokaci.

Karanta Wannan  Yadda ake danwake

ADAMSY’S KITCHEN AND MEDICINE
WHATSAPP:
08051115383, 08036066553,
08093651535..

Dauko ganda, kayan ciki, kifi, kayan kamshi, sinadarin dandano ki zuba a ciki ki juya, ki rufe tukunya na dan wani lokaci, sai ki kawo dafaffafen kwan ki sa ki juya.

Ki dauko alayyahun nan ki sa a ciki ki juya, ki kuma kawo ganyen kori da lawashi ki sa ki juya ki dan bar shi ya turaru kadan sai ki sauke.

Ana iya cin wannann miyar da kowane irin tuwo, kamar tuwon shinkafa, da kuskus da dai sauransu. A ci dadi lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *