Wednesday, January 15
Shadow

Yadda ake yin pizza

YADDA AKE YIN PIZZA
Abubuwan Da Ake Bukata:

  1. Nikakken Nama
  2. Flour
  3. Albasa
  4. Yeast
  5. Tafarnuwa
  6. Mai
  7. Maggi
  8. Tumatur
  9. Farin masoro

  10. Yadda Ake Yi:

Zaki Kwaba Flour ki da yeast da maggi da farin masoro da mai ko butter ki ajiye sai ya kumburo kaman kwabin cin~cin sai ki dauko nikakken namanki da kika soyashi sama~sama da maggi da garin tafarnuwa sai ki aje ki dauko flour nan ki gutsira ki murzata da dan tudu idan kuma falai~falai kikeso to sai kin gama murzawa sai ki debi wannan hadin ki zuba akai ki dauko tumatur dinki da kika jajjaga tare da attaruhu da albasa ki zuba akai ko kuma ki zuba kafin naman, sai ki murza wata flour kamar waccan sai ki rufeta dashi ki dora a farantin gashi bayan kin shafeshi da mai, ki barshi kamar 20 minutes sai ki fidda ita za kiga ya gasu yayi ja yayi kyau, sai ki samu wukarki me kaifi kiyi mata kalar yankan da kike so.

Karanta Wannan  Yadda ake dafa taliya da doya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *