Wednesday, January 15
Shadow

Yadda manoma ke kwana a gonaki domin gadin amfanin gonarsu a jihar Yobe

A Najeriya, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda tsananin sata ke tilasta manoma fara kwana a gonakinsu domin gadi saboda yadda ɓarayi suka addabe su da satar amfanin gonakinsu.

A jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabas – inda aka samu rahoton ƙamarin lamarin – manoma da dama sun fara tarewa a gonakinsu ne musamman a cikin dare, wasu kuma aka tilasta musu su girbe amfanin ko da kuwa ba su isa girba ba saboda gudun kada su yi asara baki ɗaya.

Daga cikin ƙananan hukumomin da matsalar ta fi ƙamari akwai Gujiba, da Damaturu, da Gashuwa, da sauransu.

Lamarin ya kai ga wasu manoman na ɗaukar hayar mutane domin taya su gadi a gonakinsu, inda suke kwana ido biyu.

Wannan matsala ba za ta rasa nasaba da yanayin da ake ciki a Najeriya ba na tsadar rayuwa, da hauhawar farashin kayan masarufi, wanda ya ƙaru tun bayan janye tallafin man fetur da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi, wanda kuma ya jawo hauhawar farashin fetur ɗin.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya ta baiwa masu boye da dalar Amurka a gidajensu watanni 9 su fito da ita

‘Dole mu kwana ko mu rasa amfaninmu’

A game da yadda lamarin ya yi ƙamari, Malam Zakari Adamu shugaban ƙungiyar adalci ta arewa maso gabas ya tabbatar da lamarin ya so musu da ba-zata, inda ya bayyana wa BBC cewa shi kan shi sabon salon na sace-sacen amfanin gonar ya shafe shi matuƙa.

A cewarsa, “Ta kai ta kawo yanzu mutum dole ya riƙa zuwa gonarsa yana kwana, inda mutum ke yin kwanaki yana zuwa kwana a gonar. Matuƙar hatsinka ya isa girbi, dole ka koma kwana a can, idan kuma ba haka ba, to lallai manomin zai wayi gari an yanke masa amfanin gonarsa,” in ji shi, inda ya ƙara da cewa lamarin yana jefa manoma cikin tashin hankali.

Malam Zakariya ya ƙara da cewa ɓarayin sun fi satar kayan hatsi, “irin su gero da dawa. Ka san yanzu lokaci ne na aikin dawa. Don haka yanzu an fi satar dawar sosai da ire-irensu,” in ji shi.

Karanta Wannan  Shin matakan tsuke bakin aljihun CBN na tasiri wajen rage hauhawar farashin kaya a Najeriya?

Ya ƙara da cewa lamarin ya ƙara ƙamari ne saboda yadda ɓarayin suke satar tamkar za su ƙwace kayan amfanin gonar daga manoman, “wanda ya sa dole mutane su je gadin gonakinsu.”

Shi ma Malam Umar Matazu a jihar Yobe, ya ce tun lokacin da ya taso ya tsinci kansa a harkar noma, amma bai taɓa ganin matsalar da ta ɗaga musu hankali irin wannan ta satar ba.

A cewarsa, “Yanzu haka da nake magana, wakena yana yaɗo ne, amma dole an nome shi duk da cewa bai kai lokacinsa ba, amma dole mu girbe saboda tsabar satar da ake mana.” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Yanzu haka maƙwabcina, duk da yana da lalurar rashin ji sosai, yanzu dole ya ɗauki wasu mutum biyu su raka shi domin su kwana a gonar tare domin gadi.”

Karanta Wannan  Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya daga zaman majalisar zartaswa har sai abinda hali yayi saboda mutuwar shugaban sojojin kasa na Najeriya

Yadda lamarin ke shafar manoman

Manoman sun koka kan yadda suka ce wahalar da suka sha wajen noma, tana neman tafiya a banza saboda satar, inda suka ce ɓarayin na yunkurin durƙusar da su, sannan suka ce yawancin ɓarayin ma ko an kama su, babu abun arziki da za a ƙwata a hannunsu saboda yanayin da suke ciki na talauci0.

“Galibi waɗanda suke satar hatsin nan za ka ga idan an kama su, sai ka ga duk talakawa ne da suke cikin tsananin rashi, wasu ma ko abin da za su ci ba su da shi,” in ji shi.

Malam Umar ya ce satar ta jefa su cikin damuwa. “Ai dole rayuwarmu za ta tawaya idan aka sace mana abin da muka sha wahala muka noma. Amma babban abin da ya jawo wannan matsalar ita ce yanayin da ake ciki tsadar rayuwa. Mu dai haka muke tunani, musamman idan ka ga waɗanda aka kama suna satar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *