Wednesday, January 15
Shadow

Yadda Yaro Ya Jagoranci Ķìsàn Mai Gidanśa Tare Da Ƙòñe Gawar Šà À Kano

Daga Anas Saminu Ja’en

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wasu Matasa Uku da suka haɗar da Aliyu Adamu da Mubarak Abdussalam da kuma Sadik Sunusi da ake zargin su da kisan wani Matashi Dahiru Musa me shekaru 32 a Unguwar Gaida ƴan Kusa, bayan sun gayyace shi har gida suka ba shi shinkafar bera a cikin abinci, tare da caççaka masa wuka har ya mutu daga ƙarshe suka bankawa gawàŕ sa wuta.

Kakakin rundunar ƴan Sanda SP Abdullahi Haruna Kiyawa, Ya wallafa Labarin.

YADDA ABUN YA KASANCE: Wani ɗan uwan sa da muka sakaye sunan sa, Ya bayyana wa Anas Saminu Ja’en abun da ya faru da Matashin Dahiru Musa wato Alh. Senior mai kimanin shekaru 33 mazaunin Layin Gidan Tsamiya da ke Ɗorayi Gidan Dakali a jihar Kano, Ya ce a ranar Lahadi 29 ga watan Satumbar 2024 Marigayi Baba Alhaji bai kwana a gida ba ake ta tunani ina ya je tunda shi baya wuce ƙarfe 10:00 zuwa 11:00 na dare ya dawo gida, Sai da gari ya waye safiyar Litinin aka shiga neman sa aka ce da suwa suka fita ranar Lahadi sai aka ce akwai yaron sa mai suna Aliyu Walantse ɗan kimanin shekaru tare suka fito, Saboda shi Marigayi Dahiru sana’ar sa ita ce saye da sayar da Filaye da Gonaki ko Gida kuma mai gidan shi Aliyun ne domin tasu ta zo ɗaya, Domin hatta wasu muhimman takardun sa na filaye ko gona shi ne ke ajiye da su, To bayan an kira wayar Dahiru har an gaji sai aka kira ta Aliyu sai aka ji ta a kashe.

Majiyar ta mu ta ci gaba da faɗin, To akwai yayan Marigayin sai ya ɗauki abokin sa suka tafi gidan Aliyu a can Ƴan Kusa da ke yankin ƙaramar hukumar Kumbotso, Suna zuwa shi Aliyu zai fita suka ce mun wurin ka muka zo! Dama jiya Lahadi an ce kai ne mutun na ƙarshe da aka gan ku tare da Alhaji? Ya ce Eh! sun je gidan yayar Marigayin a Ɗanbare can hanyar sabuwar Jami’ar Bayero da ke Kano amma bayan sun gama ya zo ya ajiye shi a Kabuga – Inji shi Aliyu yaron Marigayin yake faɗawa yayan Dahiru

Bayan sun dawo gida sai aka kira mijin ita yayar Marigayin bayan an tambaye shi? Ya ce bayan sun gama cin Abinci sai shi mijin yayar tasa ya ce za shi Rijiyar Zaki, Idan hanyar suka yi su rage masa hanya tunda a Babur suke. Aliyu ya ce ai Sabon Titin Panshekara za mu yi tunda Ƴan Kusa za mu je ba Kabuga ba! Sai Marigayin Alh. Senior ya ce da Aliyu ka ɗauke shi ka kai shi sai ka dawo mu tafi.

Karanta Wannan  'Yan Bindiga sun kashe mutane 12 ciki hadda 'yansanda 7 a jihar Zamfara

Anas Ja’en a binciken da ya yi da bin labarin kisan shi Ɗahirun, Tun farko akwai wani Kango da shi Aliyu ya kawowa Marigayi Dahiru talla, Sai mai gidan shi Senior ya ce bai yadda da sahihancin takardun Kangon ba. Aliyu ya matsa lamba sai Marigayi Senior ya sayi wurin har yake cewa na abokin sa ne ya matsu ya sayar saboda yanayin da ake ciki zai bar ƙasar ne, Ashe duk faɗa yake ba na yaron da ya faɗa ba ne Kangon.

A ranar Lahadin 29 ga watan Satumbar 2024 ne Alh. Senior ya yi fitar ƙarshe da yamma, Sai Aliyu ya kira shi a waya ya ce da shi ya fito titin Gidan Dakali su je sukai takardun Kangon nan sai Senior ya ce ya zo loko ya same shi Aliyu ya ce ya fito ba zai samu shigowa ba, Baya ya fita daga gida a wannan lokacin aka kyautata zaton sun kashe Alhaji nan gida duk ba a sani ba, To fa bayan mun sanar da jami’an tsaro ƴan sanda abun da ke faruwa ne sai suka hau bincike akan lamarin a nan fa shi Aliyu Walantse ya shiga cikin mutanen da ake zargi da kisan Marigayi Alhaji kuma yaƙi bayani.

Ya sanar da Anas cewa babban abun takaici sai da aka je babban sashin bincike na hukumar ƴan sandan jihar Kano, Ranar da aka cika kwanaki huɗu aka kira wani da muka sakaye sunan sa wanda da wayar sa aka kira Marigayi da ita cewar za’a kawo kuɗin fili, Kwatsam sai aka samu labarin an ga wata gawa a Ƴan Kusa. Ashe Baba ne bayan an kashe shi kuma aka ƙone gawar sa.

Bayan an kira a ce ga Gawa a Ƴan Kusa, Sai yaron Aliyu ya ce gawar Alh. Senior ce shi ne ya kashe shi ya ai ni ne na kashi shi, Da aka tambaye mai yasa? Ya ce ɗaukar sa na a Babur daga gidan Dakali na kira wani abokina Mubarak ya zo muka je gidana a Ƴan Kusa na dafa masa INDOMI na saka Shinkafar Ɓera muka ba shi ya ci jinin sa yana da ƙarfi sai ya ringa yin amai ya ce cikin sa na ciwo duk da haka muka fesa masa wata Hoda, A ƙarshe sai ya ce Mubarak ya riƙe shi ya ringa caka masa WUKA a ƙirjin sa suka ɗaure Marigayi Alhaji Senior har sai da ya mutu.

Karanta Wannan  Ya kamata majalisar tarayya ta yi dokar da zata hana 'yan siyasa saukewa da wulakanta Sarakai>>Sheikh Dahiru Bauchi

Ya ƙara da cewar, A lokacin da suka tabbatar ya rasu ne sai suka fito da gawarsa waje a cikin Buhu cikin wasu ciyayi da ke kusa da gidan shi Aliyu suka ƘONE ta – Inji Aliyu

YADDA SUKA TAFKA TA’ADDANCI: Sai ranar Litinin da safe akwai mai gidan shi Marigayi Alhaji Senior da ya hana shi sayan Kangon da aka kawo talla, suka yi masa waya cewar ya kawo kuɗin wannan Kangon sai ya ce ina shi Ɗahiru ku bashi wayar mu yi magana suka ce yana ciki Kangon bari su kai masa kawai sai suka kashe ta. To ba a ƙara kunna wayar ba sai da yamma na ce bari na kira Alhaji duk da jikina ya bani cewar ya rasu bayan na ji ta yi ƙara aka ɗaga sai aka kashe ba wanda ya yi magana na ke cewa wayar Alhaji ta yi ƙara da na sake kiran ta kusan sau huɗu sai muka ji ta a kashe, Ashe kashe ta da aka yi Aliyu ya tura da layin shi Marigayi Kurfi da ke jihar Katsina saboda ya kawar da hankalin mutane.

DALILIN KISAN ALHAJI SENIOR: Majiyar da shaƙiƙin Dahiru ya faɗa mana shi ne, Aliyu da bakin sa ya ke faɗar cewar abun da yasa ya kashe shi akwai wasu muhimman takardun Filayen sa suna cinikin wata gona sai ya bawa Aliyun ajiyar su, Ya baya so a taɓa su idan suka gama cikin waccan gonar sai na sayar da su abun da ke hannu na sai mu ciki mu biya kuɗin gonar can. To wai waɗannan filayen shi ne abun da ya sa Aliyu yasa a ransa yana son ya mallake su ya sayar da su saboda takardun da dukkanin wasu muhimman kadarorin Marigayi Alhaji Senior suna hannun sa, Wannan shi ne ƙarshen abun da ya faru da dalilin sa na kashe mai gidan sa saboda duniya.

Karanta Wannan  Kuma dai: Kasar Israela bata daddara ba, ta sake kai harin da ya kashe sojan kasar Iran

Matar Aliyu da ake zargi da kisan Marigayi Alh. Senior, Ta bayyana cewar bayan ta dawo gida ta tarar da gidan ta kaca-kaca a hargitse ɗakin ta sai shi Aliyun yake faɗa mata cewar su abokan sa ne su Mubarak da suka zo tun safe suka yi wasan banza shi yasa taga gidan haka sai ta bar maganar.

Aliyu ya ƙara bayyana cewar ba ranar suka ƙona Marigayi Alh. Senior ba, Ashe tun ranar farko da aka tsare shi bayan wani abokin sa ya je wajen ƴan sanda inda ake tsare da Aliyu sai ya bawa abokin nasa umarnin cewa ya je ya ƙona gawar Alh. Senior yana ganin ko an tsinci gawar zai iya fita daga zargi idan ya yi haka, Kuma shima wanda ya ƙone gawar da mutum biyu na baya Aliyu da Mubarak suna hannun ƴan sanda sai kuma sun baza komar su wajen ganin sun cafke ƙarin mutum ɗaya matuƙin Adaidai Sahu da ya taimakawa masu laifin ta ɓangaren kalle musu hanya da kai su wurin da aka aikata kisan, Wanda dukkanin su mazauna Mandawari da ke yankin ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano.

A ƙarshe muna godiya sosai ga duk Jami’an tsaron da hukumar ƴan sandan jihar Kano domin ganin irin ƙoƙari da suka yi na tabbatar da sahihin bince tare da kama wanda ake zargi, Kuma za mu manta da al’umma daga sassa daban-daban na jihar Kano wanda muka sani da wanda ba mu sani ba da suka taya mu alhini da addu’o’in wanda ita ce silar tonon asirin abun da ya faru, Kuma muna fatan gwamnati da masu ruwa da tsaki su tabbatar da sun ƙwato mana haƙƙin ɗan uwan mu kar jinin sa ya tafi a banza a hukuta masu laifi daidai da abun da suka aikata, Allah ya gafarta wa Baba Alhaji yasa aljanna makomar sa, Amin.

Sai a ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba 2024 muka yi jana’izar sa a Gadon Ƙaya kamar yadda addinin Musulinci ya tanadar, Allah ya gafarta masa. Ya sa aljanna makomar sa ya ci gaba da kare al’ummar musulmai da sharrin mutum da aljan, Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *