Friday, December 5
Shadow

‘Yan Bìndìgà sun kai hari wani sansanin sojojin Najeriya dake jihar Zàmfara inda suka kori sojojin suka konashi, sojojin sun koka da rashin makamai

Rahoto daga jihar Zamfara na cewa, ‘yan Bindiga sun kai wani mummunan hari akan wani sansanin sojojin Najeriya dake Jangebe inda suka koneshi.

Sun kai harinne da misalin karfe 3 na daren ranar Asabar.

A garin Jangebe ne dai ‘yan Bindigar suka taba sace ‘yan mata daliban makaranta dake da shekaru tsakanin 10 zuwa 17 a ranar 26 ga watan Fabrairu na shekarar 2021.

Harin ya farune a makarantar kwana ta mata me suna Government Girls Science Secondary School.

Majiyar tace sojojin basu da kayan aiki kuma ta kara da cewa soja daya ya jikkata kuma an garzaya dashi Asibiti.

Karanta Wannan  El-Rufai na son kawo rudani a kasarnan>>Inji Wata Kungiyar Arewa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *