A ranar Alhamis, ‘yan Kasuwa a Kano sun yi zanga-zangar rushe shaguna 5000 a IBB way.
An yi rusau dainne ranar Laraba bayan cikar wa’adin awanni 48 da aka baiwa masu shaguna su kwashw kayansu kuma su tashi.
Da yawa cikin wadanda lamarin ya shafa aun zauna a wajan inda suka ce ba zasu tashi ba inda kuma suka rika zagin gwamnatin jihar ta Kano.
Shuwagabannin kasuwar sunce sun shafe shekaru 18 suna zaune a wannan kasuwa tun bayan da aka basu wajan ta hannun Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim
Rusau din ya zo kwanaki 4 kamin sallah a yayin da mutane ke rububin sayayyar sallah.