Friday, December 5
Shadow

‘Yan kwallon Najeriya sun yi fushi sun dawo gida Najeriya ba tare da buga wasa da kasar Libya ba bayan da kasar ta Libya ta wulakantasu ta barsu a filin jirgi

‘Yan kwallon Kafa na Najeriya Super Eagle sun yi fushi sun dawo gida Najeriya bayan da kasar Libya ta wulakantasu.

A baya dai mun kawo muku yanda kasar Libya ta karkatar da jirgin saman Najeriya da gangan zuwa wani gari na daban dake da tazarar tafiyar awanni 2 tsakaninsa da inda zasu buga wasa da kungiyar kwallon kafar ta Libya.

Hakan yasa ‘yan wasan Najeriyar suka kwashe awanni 13 a filin wasan ba tare da kulawa ba.

A karshe dai bisa umarnin hukumar kwallon kafa ta Najeriya, ‘Yan kwallon Na Najeriya sun dawo gida ba tare da buga wasa da kasar ta Libya ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Bakin cikin dake damuna shine har yanzu bani da aure>>Murja Kunya

Dama dai wasan na samun gurbin buga gasar cin kofin Nahiyar Africa shine zai tabbatar da zuwan Najeriya gasar da ta bugashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *