Friday, December 5
Shadow

‘Yan Najeriya 203 da suka maƙale a Libya sun koma gida

Hukumar agajin gaggawa a Najeriya ta ce ta karɓi ‘yan ƙasar 203 da aka kwaso daga Libya bayan sun kasa fitowa daga ƙasar ta arewacin Afirka.

Jim kaɗan bayan isarsu filin jirgin sama na Murtala Muhammed a Legas a jiya Litinin ne jami’an hukumar ta tarɓe su.

Jirgin kamfanin Al Buraq ne ya kwaso mutanen, waɗanda suka ƙunshi maza manya 50, mata manya 96, da yara 29, da kuma jarirai 28.

Ƙungiyar kula da ƙaura ta duniya wato International Organisation for Migration (IOM) ce ta ɗauki nauyin mayar da su gida bisa haɗin gwiwa da hukumar National Emergency Management Agency (Nema) da sauran hukumomi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda fadawan sarkin Katsina suka fasa kofar taro suka shigar da sarkin bayan da aka kulle kofar dakin Taron da aka yiwa Tinubu Maraba a jihar

Wata sanarwa da Nema ta fitar ranar Talata ta ce biyu daga cikin mutanen na buƙatar kulawar gaggawa, “kuma nan take aka kai su asibitin Ikeja domin duba su”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *