
‘Yan Najeriya da yawa ne ke zuwa bankunansu suna dakatar da alert din bankinsu da ake tura musu a duk sanda suka cire ko aka aika musu da kudin.
Hakan na faruwane saboda kudin Alert din da ake cirewa sun yi yawa.
Kwastomomi da yawa nw ke zuwa bankunansu dan dakatar da aika musu da sakon alert din.
A hira da jaridar Daily Trust ta yi da wasu daga cikin kwastomomin, sun ce kudin da ake cire musu yayi yawa shiyasa suka je bankunansu dan dakatar da aika musu da sakon.
Wasu sun ce sun kwammace a rika aika musu da sakon ta Email.