Friday, December 5
Shadow

Yan sanda sun gargaɗi yara lanana masu tuƙa Adaidaita Sahu a Kano

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi gargaɗi game da yadda yara ƙanana ke tuƙa babur mai ƙafa uku da aka fi sani da Adaidaita Sahu a birnin Kano.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Litinin ta bayyana damuwa kan yadda ƙaruwar yara ƙananan da ke tuƙa babur mai kafa ukun ke jefa rayukan mutanen jihar cikin haɗari.

Sanarwar ta ce a cikin watan Agustan nan kaɗai, an samu manyan haɗurra 16 sanadiyyar tuƙin da yaran suke yi, lamarin da yayi sanadin jikkatar mutane da dama da kuma asarar dukiya mai yawa.

‘Yan sandan sun gargaɗi jama’a da su riƙa bin ƙa’idojin tuƙi tare yin biyayya a duk lokacin da fitilar kan hanya ta nuna a tsaya ko a tafi.

Karanta Wannan  Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya auri mata ta 4, kalli Bidiyo daga wajan Biki

Rundunar ƴan sandan ta kuma ce ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kamawa da hukunta duk wanda aka samu da karya dokokin don tabbatar da tsaro da kare lafiyar al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *