
A wani rahoto da jaridar Sahara Reporters ta ruwaito ya nuna cewar, ana zargin gamayyar jami’an tsaron Nijeriya suna shirin kai mummunan hari wasu gurare guda biyar cikin muhallan yan Harkar Musulunci kamar yanda majiyar ta bayyana.
Majiyar ta kuma shaida ma jaridar Sahara Reporters yadda Gamayyar jami’an tsaron suke ta tattaunawa da sauran jami’an a karkashin kasa, suna faɗa musu su kwana cikin shiri domin gudanar da aikin da zasu yi a cikin daren Litinin da misalin karfe 2 na daren nan.
A makon data gabata ne dai aka yi jana’izar wasu cikin mutanen da sojoji suka kashe masu gudanar da jerin gwano kan lamarin Palasɗinu.
Sama da mutane dari uku ne ake tsare dasu a gidajen yarin Kuje dake Abuja da kuma Suleja, wasu kuma suna hannun yan sanda kamar yanda Lauyoyin Harkar Musuluncin suka bayyana a yayin gudanar da taron manema labarai da suka yi jiya.
Source: Sahara Reporters