Wednesday, January 15
Shadow

‘Yan sanda sun kama mutum huɗu kan zargin garkuwa da mutane a dazukan Abuja

Rundunar ‘yan sandan birnin Abuja, tare da haɗin gwiwa dakarun sahen yaƙi da manyan laifuka da ‘yan sanda farin kaya, da mafarauta, sun wargaza sansanonin wasu ‘yan bindiga a ƙauyen Gidan Dogo da dajin Kweti da ke kan iyakar Abuja da Kaduna.

Cikin wata sanarwar jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ‘yan sandan birnin, SP Josephine Adeh, ta fitar ta ce bayan samun bayanan sirri, jami’an tsaron suka kai samame dajin ranar 7 ga watan Mayu, in da suka kama mutum huɗu da suke zargi.

Sanarwar ta ce mutanen da suka kama, sun faɗa wa ‘yan sanda cewa suna cikin wani gungun masu garkuwa da mutane mai suna, ‘Mai One Million’, waɗanda suke da alhakin kai hare-hare tare da garkuwa da mutane a birnin Abuja da kewaye.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya ta janye zargin ta'addanci da takewa shugaban Miyetti Allah, Bodejo

‘Samamen wanda aka samu musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu, ya tilasta wa ‘yan bidigar tserewa, inda jami’an tsaro suka ƙubutar da mutanen da ‘yan bindigar ke tsare da su”, in ji sanarwar.

‘Yan sandan sun ce sun lalata sansanonin ‘yan bidigar a lokacin samamen.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan ta ce ta sada mutanen da ta kuɓutar ɗin da iyalansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *