Wednesday, January 15
Shadow

‘Yan Sanda Sun Kwato Motar Sata, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Jigawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani mutum mai suna Mahmud Adam mai shekaru 43 da laifin satar mota, tare da gano motar kirar SUV da aka sace a karamar hukumar Gwaram.

DSP Shiisu Adam, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jigawa, ya sanar da hakan a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni, cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar, 15 ga watan Yuni.

A cewar Shiisu, kama barawon ya biyo bayan rahoton sace wata mota kirar Honda CRV mai lamba DKD 10 AG mallakin Wani Abba Yahya daga garin Gano da ke karamar hukumar Dawakin Kudu ta jihar Kano.

Karanta Wannan  Hoto: Wannan matashin ya yi garkuwa da kansa ya karbi Naira Miliyan 5 daga gurin mahaifinsa

Ya ce motar tana kan hanyar zuwa Maiduguri jihar Borno.

Ya bayyana cewa, jami’in ‘yan sanda (DPO) na Gwaram tare da tawagarsa sun tare motar kirar SUV akan hanyar Sara zuwa Darazo.

SHiisu ya ce tuni aka mika wanda ake zargin da motar da aka gano ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano domin ci gaba da gudanar da cikakken bincike.

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *